Aikin raba tagwaye a asibitin Jami'ar Maiduguri

Image caption Likitoci na kan aikin tiyata

A Najeriya yanzu haka likitoici a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri na nan na gudanar da aikin tiyatar raba wasu tagwaye maza yan kimanin shekara guda.

Likitocin sun bayyana cewar tagwayen wadanda iyayensu sun fito ne daga Karamar Hukumar Ningi jihar Bauchi an haife su ne da cibiyya daya,da kafafuwa uku da wasu mihimman sassan jikin su a hade.

Da misalin karfe takwas na safiyar yau ne lilkitocin suka fara gudanar da aikin fidar raba tagwayen wanda shine karo na farko a wanann Asibiti da ake sa ran shafe sa'oi kafin a kammala.

A watan Satumbar shekarar da ta gataba ne dai Asibitin Koyarwar na Jami'ar Maidugurin ya gudanar da aikin dashen koda na farko a Asibitin wanda kuma shine karo na farko akayi irin wannnan aiki a Najeriya ba tare da hadin gwaiwar lilitocin kasashen waje ba.