ANPP ta kaddamar da kamfe a Abakaliki

Image caption Dan takarar shugaban kasa na ANPP, Mallam Ibrahim Shekarua, gwamnan jihar Kano.

A Najeriya jam'iyyar adawa ta ANPP ta kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa, Mallam Ibrahim Shekarau a garin Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.

Jam'iyyar ta kaddamar da kamfe din ne, duk kuwa da hana gudanar da taron da gwamnatin jihar ta jam'iyyar PDP ta yi, bisa abin da ta kira dalilai na tsaro.

An dai gudanar da taron kamar yadda aka tsara. Magoya bayan Jam'iyyar daga sassa dabam-dabam a Najeriya ne su ka halarci wurin taron gangamin.

Alhaji Musa Inuwa Gana wani mai baiwa dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar shawara, ya ce taron ya zo da ba zata.

"Gaskiya mun samu dumbin magoya baya, kuma muna farin ciki da hakan." In ji Inuwa Gana.

"In Allah ya yarda dan takarar mu ba zai yi kasa a guiwa ba."

Magoya bayan jam'iyyar dai sun nuna kwarin gwuiwar cewa dan takarar su ne zai lashe zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Afrailu.