Dakarun Gaddafi na cigaba da kai hari

Dakaru a Libiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakaru a Libiya

Dakarun dake goyon bayan jagoran Libiya, Kanar Gaddafi, sun kara bude wuta da igwa da ma ta sama a garuruwan dake hannun 'yan tawaye.

Kimanin tankunan yaki na gwamnati 50 ne rahotanni suka ce sun kai hari a garin Zawiya dake kusa da birnin Tripoli.

Wani da ya ganewa idansa abinda ya faru, yace ana harbi ta ko'ina, kuma garin ya zama kamar an share shi daga doron kasa.

Gwamnatin Libiya dai ta musanta cewa dakarunta na kashe fararen hula.

Sai dai kuma wakilin BBC ya ce baza a iya tantance gaskiyar lamarin ba, saboda ba barin mutane su shiga garin.

Shugaban hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce an samu an shawo kan halin da ake ciki game da 'yan gudun hijira a kan iyakar Libiyar da Tunisia.

Mr Guterres ya shaidawa BBC cewa kimanin 'yan cirani 'yan kasar Bangladesh dubu 14 ne har yanzu ke jiran a kwashe su zuwa kasarsu.