Jama'iyu sun sa hannu kan wata yarjejeniya tare da hukumar zabe a Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta yi wani taro tare da shugabannin jamiyyun siyasar kasar, inda ta gabatar da wasu dokoki da tsare tsaren da jamiyyun za su yi aiki da su a lokacin zaben watan Afrilu, domin su sa hannu a kai.

Galibin jama'iyun da suka halarci taron dai sun sanya hannu a kundin, amma wasu sun yi haka.

jam'iyyar PDP mai mulkin kasar dai ta bayyana aniyarta ta sa hannu kan kundin ba.

Manufar wannan kundi dai shine, samun tabbaci daga wurin jamiyyun siyasar, cewa ba za su yi wani wani abu da zai yi zagon kasa ga zabenda za a gudanar ba.