'Rikice-rikice za su shafi zaben Najeriya'

Ambasada Jonnie Carson
Image caption Ambasada Jonnie Carson

Mataimakin Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afrika, Ambasada Jonnie Carson, ya ce tashe-tashen hankulan da ake fama da su a wasu sassa na Najeriya matsaloli ne da idan ba a shawo kansu ba za su iya yiwa zabe mai zuwa cikas.

Ambasada Carson ya fadi hakan ne a wata ganawa ta mussamman da ya yi da 'yan jarida a kan zaben Najeriya a ofishin jakadancin Amurka da ke London.

“Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula da rikice-rikice a yankin Naija Delta; ga kuma rikice-rikicen addini da kabilanci a Jihar Filato, musamman a birnin Jos da kewaye; kuma muna sane da ayyukan Boko Haram a wasu sassa na arewacin kasar.

“Dukkan wadannan matsaloli guda uku ka iya kawo cikas ga yunkurin shiryawa da gudanar da zabe.

“Haka nan kuma muna sane da wadansu matsaloli da suka dabaibaye wadansu jihohi—wadannan matsalolin na bukatar karin kulawa da taka-tsantsan idan dai ana so a gudanar da ingantaccen zabe.

“Wadannan kalubale ne; to amma muhimmin abin dubawa shi ne yadda za a ciyar da Najeriya gaba”.

Mataimakin Sakatariyar Harkokin Wajen Amurkan ya kuma ce ya kamata Najeriya ta kaucewa irin zaben 2007 wanda ya ce cike yake da kurakurai.

“Zabukan shugaban kasar na 2007 na cike makil da kurakurai.

“'Yan Najeriya kalilan ne suka kada kuri'unsu a zabukan na shugaban kasa saboda takardun zabe sun isa kasar a makare”.