Yau ake bikin Ranar Mata ta Duniya

Mata a Falasdinu yayin bikin Ranar Mata
Image caption Mata a Falasdinu yayin bikin Ranar Mata

A yau ne ake bikin Ranar Mata ta Duniya—ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba irin matsalolin da matan ke fuskanta wadanda suka hada da na siyasa, da tattalin arziki, da ilimi, da kuma zamantakewa a cikin al'umma.

Majalisar Dinkin Duniyar ta jaddada muhimmancin wannan rana da cewar za ta iya fadakar da kasashen duniya domin su kula da halin da matan suke ciki, tare da kokarin kawo sauyi.

A tarihin kasar Brazil ba a taba samun mata masu yawa rike da muhimman mukaman gwamnati kamar wannan karon ba.

Wannan kuma tasiri ne na zaben Dilma Rousseff a matsayin shugabar kasa.

Baya ga ita Dilma Rousseff, wadda ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kasar Brazil, tara daga cikin ministocin kasar talatin da bakwai ma mata ne.

Wannan kuma shi ne karo na farko da aka taba samun mata masu yawa haka a majalisar ministocin kasar; yawan nasu kuma ya ninka lokacin tsohon shugaba Lula da Silva sau biyu.

Gwamnatin tarayyar kasar dai ta kaddamar da wani kamfe mai taken "mata za su iya zama duk abin da suke so".

Sai dai duk da zaben Dilma Rousseff, masu fafutukar kare hakkin mata na ganin akwai bukatar a ba su karin dama.

A cewar jami'ar wata kungiyar kare hakkokin mata ta kasa-da-kasa, Mirian Nobre, yana da matukar muhimmanci a samu sauyi a rayuwar mata ta yau da kullum; saboda haka ne suke sa ido a kan abin da Dilma Rousseff ta ke yi don inganta rayuwar mata.

Mis Nobre ta kuma kara da cewa ko da yake ci gaba ta fuskar siyasa abu ne mai muhimmanci, har yanzu mata da dama na fama da kalubale ta fuksar tattalin arziki.

A Najeriya kuwa, inda ake fuskantar babban zabe a wata mai zuwa, kamar sauran kasashen Afrika, mata cewa suke yi ba sa samun damar da ta kamata a harkokin da suka shafi makomar alumma, kuma suna zargin cewa maza na kasancewa tamkar shinge ga cimma burinsu na kaiwa ga manyan mukamai a kasar.

Hajiya Rabi Musa kusa ce a kungiyar kare hakkokin mata ta WRAPA, ta kuma shaidawa BBC cewa a wannan siyasar, mata a Najeriya sun samu ci gaba don kuwa an samu 'yan takara mata da dama.

"Wannan a zabe dai na 2011 mata sun yi rawar gani; don a jihohin ma da mata yawanci ba a san suna fitowa ba (jihohi irin namu na can arewa, su Katsina, su Zamfara) mata sun fito sun nuna sha'awar cewa su ma suna so a yi da su.

"Cikin ikon Allah mun samu mata fiye da dari biyar da suka fito a duka jihohin kasar nan; har ma akwai wadanda ke neman gwamna duk mun samu", in ji Hajiya Rabi.

Sai dai, a cewarta, matan da suka samu tsallake zaben fitar da gwani da kyar ba su wuce dari da tamanin ba.