Jirgin tawagar ACN ya kuskure hadari

A Najeriya daya daga cikin jiragen dake dauke da tawagar yakin neman zaben dan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam'iyyar adawa ta ACN, Malam Nuhu Ribadu ya yi wani karamin hadari a filin jirgin sama na garin Bauchi, inda suka je yakin neman zabe a gabanin zabukan da za a yi a watan Afrilu.

Jirgin dake dauke da mataimakin dantakarar shugaban kasa na jam'iyyar ta ACN, Fola Adeola, da wasu mukararraban Malam Nuhu Ribadun, ya ci karo da wasu dabbobi da suka hada da raguna yayin da yake sauka a filin jirgin, yayin da shi kuma jirgin da shi Malam Nuhu Ribadun ke ciki, ya yi ta shawagi a sama na tsawon lokaci kafin daga bisani ya samu damar sauka.

Malam Ibrahim Modibbo, daraktan watsa labarai na kungiyar yakin neman zaben Malam Nuhu Ribadu, ya ce suna zargin makarkashiya aka shirya masu.

To sai dai kuma mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara kan harkokin siyasa Malam Abdulmmumini Kundak, ya musanta zargin duk wani sakaci ko kuma zagon kasa daga bangarensu.

Wani jami'i a filin jirgin saman wanda bai so a ambaci sunansa, ya bayyanawa wakilin BBC Ishaq Khalid cewa dalilin da ya sanya dabbobi suka shiga filin jirgin shi ne rashin katange filin jirgin amma ba ganganci ne su ma'aikata suka yi ba.

Ga alama dai kace-nace tsakanin gwamnati da 'yan adawa a Najeriya zai ci gaba da wakana yayin da aski ke zuwa gaban goshi a yakin neman zabe dake tafe a kasar.