Dakarun Kanar Gaddafi sun kwace garin Zawiyya

Shugaba Gaddafi na LIbya Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Shugaba Gaddafi na LIbya

Gidan talabijin na kasar Libya ya nuna wasu hotunan magoya bayan Shugaba Gaddafi suna ta murna a tsakiyar garin Zawiyya, bayan fatattakar da suka yi ma 'yan tawaye a fadan da aka kwashe kwana da kwanaki ana tabkawa.

Da wuya dai a tantance gaskiyar lamarin tun da ba'a yadda 'yan jaridar kasashen waje shiga garin na Zawiya ba wanda ke yamma da birnin Tripoli.

Wakilin BBC ya ce sahihan rahotanni daga garin sun ce an kashe mutane da dama ciki har da fararen hula.

Wani likita a garin na Zawiyya ya ce akalla mutane arba'in aka kashe a fadan na yau.

Yayin da kasashen duniya ke tunanin ko a hana jiragen gwamnatin Libya yawo a sararin samaniyar kasar, domin kawo karshen hare haren da suke kaiwa ta sama kan 'yan tawaye, gidan talabijin din kasar ya yi tayin tukwicin kusan rabin dala miliyan daya ga duk wanda ya kamo shugaban Majalisar Kasa ta Wucingadi, wadda masu adawa da Kanar Gaddafi suka kafa a garin Bengazi.

Shugaban majalisar, Mustafa Abduljalil minista ne a da gwamnatin Libya har sai lokacin da ya koma cikin 'yan tawayen.

Rahotanni kuma daga Brussels sun ce shugaban kasar Libya, Kanar Gaddafi zai tura wasu wakilai da za su tattauna da jami'ai daga kasashen duniya.

Ranar Alhamis da juma'a ne wakilan kungiyar tarayyar Turai da na NATO za su yi wani taro a Brussels domin auna zabin da suke da shi a kan Libyar, bayan kiraye-kirayen da ake na hana jiragen kasar yin shawagi a sararin samaniyarta: