Amurka ba za ta jagoranci mataki kan Libya ba

Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Sojojin da ke biyayya ga Shugaba Muammar Gaddafi na Libya sun shafe yinin jiya suna luguden wuta a kan garin Zawiya wanda ke hannun 'yan tawaye.

Rahotanni sun ce asibitin garin ya cika makil da mutanen da suka jikkata.

Fadan dai ya tsananta ne a garin wanda ke yammacin kasar ta Libya yayinda dakaru masu biyayya ga Kanar Gaddafi suka yi yunkurin karbe iko da garin.

'Yan adawa dai sun ce hana tashin jirage a kasar ta Libya ne kawai zai ceto rayukan mutanen kasar.

Wani mai magana da yawun 'yan adawar, Hafiz Ghoga, ya shaidawa BBC cewa hana tashin jiragen zai kubutar da al'ummar kasar daga luguden wutar da dakarun Gaddafin ke yi a kan garuruwan da ke hannun 'yan tawaye.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce Majalisar Dinkin Duniya ce kawai za ta iya yanke shawarar hana tashin jiragen sama a kasar ta Libya.

“Akwai yunkurin da kasashen duniya ke yi yanzu haka.

“Kuma mun yi amanna cewa abu ne mai muhimmanci wannan yunkuri ya kasnace ba a karkashin jagorancin Amurka ko kungiyar tsaro ta NATO, ko Tarayyar Turai ba.

“Akwai bukatar yunkurin ya kasance ya samu amincewar kasashen duniya, to amma har yanzu akwai kasashen da ke adawa da matakin”, in ji Misis Clinton.

Karin bayani