An fasa muhawarar 'yan takarar shugabancin Nijar

Zaben Nijar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Muhawara sai wani jikon

A jamhuriyar Nijar, dan takarar jam'iyyar MNSD-Nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, ya janye daga muhawarar da aka shirya yi a kafofin watsa labarai, tsakaninsa da abokin hamayyarsa na PNDS-Tarayya.

A taron manema labaran da ta kira yau, hukumar sadarwar kasar, ONC, ta ce ta soke muhawarar ce, saboda Alhaji Seyni Oumarou ya ce ba zai halarta ba, saboda kurewar lokaci.

A ranar Asabar mai zuwa ce yake shirin fafatawa da Alhaji Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS Tarayya, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Fasa muhawarar ya sanya 'yan kasar ba za samu ganin muhawarar da wasunsu ke ta dokin gani ba.