'Yan adawa na sukar takarar Jonathan

Image caption Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan.

A Najeriya, yayinda babban zaben kasar ke karatowa, muhawara sai zafafa take yi a tsakanin jam`iyyun siyasar kasar, saboda jam`iyyar adawa ta Social Democratic Mega Party ta ce rainin hankali ne shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya sake neman jagorancin Najeriya a babban zaben da ke tafe.

Jam'iyyar ta ce Shugaba Jonathan bai tabuka wani abin kirki ba a yanzu haka da ragamar shugabancin kasar ke hannunsa.

Jam`iyyar adawar ta ce lamarin tsaro sai ci gaba da tabarbarewa yake yi a kasar, ga kuma matsalar talauci da ta jefa rayuwar al`umma cikin kunci, don haka gwamnatin PDP ta gaza.

Amma gwamnatin a nata martanin, ta ce shugaba Goodluck ya yi rawar-gani, sai dai gabar siyasa ta hana masu adawa gani.

Jam`iyyar adawa ta Social Democratic Mega Party ta ce bai kamata `yan Najeriya su sake zaben jam`iyyar PDP mai mulkin kasar a watan Afrilu mai zuwa ba, saboda babu abin da ta yi musu a cikin shekaru goma sha biyun da suka wuce illa bata lokaci.

"Kuma in dai auren fari shi ne sadakin na gaba, kamar yadda `yan magana ke cewa, to bai kamata a sake danka wa shugaba Goodluck Jonathan ragamar shugabancin Najeriya ba." In ji Dr Sadik Umar Abubakar na jam'iyyar Social Democratic Mega Party.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin shugaba Goodluck din, wadda jam`iyyar PDP ta kafa ta ce ba za a yi mata adalci ba idan aka ce sam-sam ba ta da wani abin yabawa, musamman ma idan aka yi la`akari da dimbin matsalolin da ta gada.

"Kuma ko ba komai ta kama hanyar magance manyan matsalolin da suka fi damun `yan kasar, don haka ita ce ta fi dacewa da ci gaba da shugabancin kasar saboda a samu dorewar ayyukanta da ta ce na alheri ne." In ji Mista Labaran Maku ministan yada labaran kasar.

Tun komawar Najeriya ga mulkin demokuradiyya, wato sama da shekara goma sha biyu kenan jam`iyyar PDP ke mulkin kasar, kuma irin wannan caccaka da sukar da jam`iyyun adawa ke yi wa PDP ba sa rasa nasaba da ikirarin da suke yi cewar a wannan tsawon lokacin Najeriyar ta samu kudin shiga mai yawan gaske daga mai, amma duk haka gwamnatin ba ta iya cire akasarin `yan kasar daga kangin talauci ba, kasancewar mafi yawansu, kamar yadda bincike ya nuna na rayuwa ne da kasa da dala guda a kowane wuni.

Kodayake jam`iyyar PDPn ta ce tana bakin kokarinta, `yan adawa ne kawai ke fadar son-ransu, saboda na waje gwanin kokawa ne.