Ana gabatar da bayanan karshe a shari'ar Charles Taylor

Lauyan dake kare tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, ya fara gabatar da bayanansa na karshe a shari'ar da ake masa a Hague.

Mr Courtenay Griffiths ya ce shari'ar na da nasaba da siyasa, ya kuma zargi mai shigar da karar da lalata tsarin shari'ar kasa da kasa ta yadda ya mai da ita tamkar wata sabuwar hanyar mulkin mallaka na wannan karnin. Mr. Griffiths yace mun lura cewa duk wanda akewa shari'a ko yake jiran aimasa shari'a a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ko kasan dan ina ne? Afirka.

Ana zargin Mr Taylor da aikata laifukan keta hakkin Bil adama, ta hanyar baiwa 'yan tawayen Saliyo inda shi kuma yake samun demon.

Mr Taylor dai ya sha musanta wannan zargin.