Sabon rikici ya barke a Tafawa Balewa

Rahotanni daga jihar Bauchi a Nijeriya na cewa wani sabon rikici ya barke a garin Tafawa Balewa da kuma kauyen Gitel wanda shi ma ke yankin na Tafawa Balewa, inda hukumomi suka ce an sami hasarar rayuka da dukiya.

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi dai ta ce wasu mutane da har yanzu ba a san ko su wane ne ba suka kai hari da safiyar yau a garin na Tafawa Balewa , kafin daga bisani a ci nasarar korar su.

Yankin na Tafawa Balewa dai ya dade yana fuskantar tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci, da kuma addini, inda ko a watan Janairun da ya gabata, mutane sama da ashirin ne suka rasa rayukansu a wani tashin hankalin.