Mummunar girgizar kasa ta afkawa Japan

Japan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Girgizar kasar ta haifar da gobara a sassa da dama na kasar

Wata mummunar girgizar kasa ta afkawa Arewacin kasar Japan, inda ta haifar da igiyar ruwa ta Tsunami wacce ta yi banna sosai.

Gidan talabinjin na Japan ya nuna hotunan gidaje da jiragen ruwa da gine-gine suna jirkice wa bayan girgizar kasar mai karfin ma'auni takwas da digo tara.

Girgizar kasar ta haifar da gobara a wasu yankuna da dama ciki har da Tokyo babban birnin kasar, inda aka ce akalla mutane 22 sun rasa rayukansu.

Lamarin dai ya afku ne da misalin karfe 5 agogon GMT. Masu nazari sun ce ita ce girgizar kasa mafi muni da ta afku a tarihin kasar.

Damuwa a wasu yankunan

An yi gargadin ballewar Tsunami a Yankin Pacific ciki harda Philippines da Indonesia da Taiwan da Hawaii da kuma kasashen Rsha da Arewaci da kuma Kudancin Amurka.

An ga motoci na kokarin tserewa igiyar ruwa a sassa da dama na kasar.

Gonaki da dama sun lalace a yankin Sendai, yayin da iska ta tura motoci zuwa gefen titin da jirage ke sauka a filin saukar jiragen sama na birnin.

Kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya ce a kalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu, sai dai ana saran adadin zai karu matuka.