Ana ci gaba da gwabza yaki a Gabashin Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan tawaye na yaki da Sojoji Gaddafi

A Libya ana ci gaba da gwabza yaki a Gabashin kasar, kusa da garin Ras Lanuf mai tashar mai, wanda ke hannun 'yan tawaye.

Jiragen gwamnatin kasar sun kai hari a garin Brega, wanda shi ma yake hannun masu tada kayar bayan.

Kwamitin kasashe na Red Cross ya ce, har yanzu ya kasa kaiwa ga yankunan da aka gwabza kazamin yaki a Libyar.

Dakarun Kanal Gaddafi sun ci gaba da luguden bama-bamai a kan 'yan adawa a garin Ras Lanuf.

Cin zarafi

Ma'aikatan sashen Larabci na BBC bayan sallamar su daga hannun dakarun Kanal Gaddafi, sun bayyana irin cin zalin da aka yi musu.

Ma'aikatan wadanda su ma aka kame su cikin dare, sun bayyana cewa an lakada musu duka, sannan kuma sun jiyo ife-ifen mutanen da ake gallazawa.

Sun dai bayyana cewa sun ga mutanen da suka yi mummunar jikkata a hannun dakarun Kanal Gaddafi.

A yayin da haka ke faruwa, a bangare guda kuma ana ci gaba da zafafa yunkurin diflomasiyya a kan Libya.

Wasu sun yi zaton cewa tuni gwamnatin Kanal Gaddafi za ta saduda, ta bada kai bori ya hau.

Hana zirga zirgar jiragen sama

Amma fargabar cewa sojoji da dama na yin biyayya gare shi, da kuma ci gaba da kai hari da ake yi a garuruwa da kuma wuraren da al'ummar farar hula suke, kasashen duniya na ci gaba da kiran a dauki mataki.

Kwamitin kasashen dake yankin tekun Pasha dai ya amince da a saka haramcin hana zirga-zirgar jiragen sama a Libya, da zummar dakatar da ta'asar sojin saman dake yiwa Kanal Gaddafi aiki.

Wannan kuma wani batu ne da kungiyar tsaro ta Nato ke tattaunawa akai.

Kasashen nahiyar Turai kuma na duba batutuwan da suka shafi rayuwar bil adama a kasar, musamman ma bayan da kungiyar agajin Red Cross ta bayyana cewa bangaren kadai da ta iya samun damar zuwa domin agazawa shi ne gabashin kasar.

Shugaban Kungiyar Red Rross Jakob Kallenberger ya bayyana cewa akwai mutane da dama musamman a bangaren Yammacin kasar da ke bukatar agaji amma ba ta da damar kaiwa gare su:

"Bamu san halin da bil adama ke ciki ba a yaAn dai shnkunan dake karkashin ikon Trabulas." in ji Kallenberger.

"An shaida min cewa komai na tafiya kamar yadda ya kamata, kan cewa asibitoci na aiki, don haka babu bukatar kungiyoyin agaji.

"Abin da aka shaida mana kenan, amma dai duk da haka muna cikin damuwa, domin muna so mu tabbatar da haka da kan mu."

Wani batu da kasashen turai ke dubawa shi ne na kara sakawa Libya takunkumi ta fuskar tattalin arziki, baya ga wanda aka saka na haramtawa Kanal Gaddafi da mukarrabansa taba dukiyoyinsu da ke waje.

A yanzu haka dai ana tunanin sabon takunkumin zai kunshi duk wadansu bangarori da ka iya tallafawa kasar da Kudade, kamar misali jarin da kasar ke dashi a wadansu bankunan Turai da kungiyar kwallon kafa ta Juventus da kuma wasu kamfanoni.