An kammala yakin neman zabe a Jamhuriyar Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron gangamin yakin neman zabe Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, da misalin karfe goma sha biyu na daren jiya alhamis ne aka kammala yakin neman zaben shugaban kasar zagaye na biyu wanda za'a gudanar a gobe Asabar.

'Yan takara biyu ne dai zasu fafata, wato Alhaji Seyni Umarou na jam'iyyar MNSD-Nasara, mai fatan ci gaba da aikin gina kasa da ya ce ya gada daga tsohon shugaba Mamadou Tanja, da kuma Alhaji Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS-Tarayya mai neman kawo sauyi.

Hukumar zaben kasar dai ta ce ta kammala dukkan shirye shirye na ganin an gudanar da ingantacce zabe ba tare da an fuskanci wasu matsaloli ba.

Zaben dai shi ne na karshe a zabubbukan da aka gudanar a kasar, a kokarin da ake yi na mayar da Jamhuriyar ta Nijar bisa turbar demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.