Japan ta ce ba hadarin tururin nukiliya

Hukumomin kasar Japan sun nemi kwantar da hankali game da fargabar da ake nunawa ta yuwuwar narkewar makamashin nukiliya, bayan fashewar abubuwan da aka samu a wata tashar samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya, dake arewacin kasar.

Hadarin ya auku ne, kwana guda bayan bala'in girgizar kasa da ambaliyar teku ta tsunami da suka afka ma kasar ta Japan.

Hukumomin na cewa ba a samu karuwar burbushin sinadarin nukiliya ba, tun bayan fashewar abubuwan a tashar makamashin nukiliyar ta Fukushima.