Nijeriya na goyon bayan tumbuke Gbagbo

Wani kakakin Alassane Ouattara - watau mutumin da kasashen duniya suka ce shi ne ya lashe zaben shugabancin Cote d'Ivoire na watan Nuwamba - ya shaida wa BBC cewa, Najeriya a shirye take ta goyi bayan daukar matakin soja akan shugaban Cote d'Ivoire din da ya ki sauka daga mulki, Laurent Gbagbo.

A cewar Toikesse Mabri, idan har mista Gbagbo ya ki barin ofis nan da makonni biyu, to kuwa kasashen yammacin Afirka za su nufi kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, inda zasu bada shawarar a yi amfani da karfin soja, domin warware rikicin siyasar Cote d'Ivoire din.

Kakakin yana bayani ne akan sakamakon tattaunawar da aka yi a Abuja, tsakanin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, da kuma Alassane Ouattara.