Larabawa sun amince da mataki kan Libya

Kungiyar kasashen Larabawa ta amince da murya daya, da ta bukaci kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya tabbatar da takunkumin hana jirage yin shawagi a sararin samaniyar kasar Libiya.

Babban sakataren kungiyar, Amr Moussa ya ce manufar daukar matakin ita ce a kare fararen hula a Libiya.

A cewar masu aiko da rahotanni, shawarar hana jiragen yin shawagi a Libiyar, zata ba kungiyar tsaron NATO da kuma Tarayyar Turai, irin goyon bayan da suka ce ana bukata, kamin a dauki duk wani mataki na soja.