'Yan siyasa sun manta da mu, in ji Fulani

Taswirar Najeriya
Image caption Fulani sun ce 'yan siyasa sun manta da su

A Najeriya, yayin da 'yan siyasa ke fafutikar yakin neman zabe, wasu Fulani makiyaya sun koka cewa, da alamu 'yan siyasar sun manta da su.

Fulanin sun ce ba kasafai 'yan siyasar ke tabo batun da ya shafi rayuwarsu a yakin neman zabe ba.

Hakan ya sa makiyayan ke fargaba cewa da wuya ribar dimokuradiyya ta kai gare su bayan zabe.

Sai dai sun yi kira ga 'yan siyasar da su maida hankali wajen inganta rayuwar makiyaya.