Majalisar dokokin Nijeria ta maida martani ga HRW

Zauren majalisar dokokin Najeriya
Image caption Zauren majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya, bangaren majalisar dokokin kasar ya ce da wuya majalisar ta iya zartar da wata dokar da za ta ba da damar kafa hukumar ladabtar da masu aikata laifukan zabe nan da babban zaben kasar mai zuwa.

`Yan majalisar dai na maida martani ne ga wani kira da Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights watch ta yi yau din nan, inda ta nemi majalisar dokokin kasar da ta gaggauta kafa irin wannan hukuma.

A farkon watan Afrilu mai zuwa ne dai za a soma babban zaben Najeriyar, amma kungiyoyin dake rajin kare demokuradiyya na fargabar cewa akwai yiwuwar zaben ya fuskanci rigingimu.