An kafa dokar ta baci a wata tashar nukiliyar Japan

Firayim ministan Japan, Naoto Kan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firayim ministan Japan, Naoto Kan

Firayim Ministan Japan, Naoto Kan, ya ce kasarsa na fuskantar wahalhalu mafiya kamari tun yakin duniya na biyu, yayinda take fadi tashin iya tinkarar mummunar barnar da girgizar kasa da kuma ambaliyar ruwan teku ta tsunamin ranar juma'a suka haddasa.

Yayinda hukumomi ke kokowar hana rugujewar tashar nukiliya ta Fukushima wadda lamarin ya shafa, an ayyana dokar ta baci a tashar nukiliyar ta 2, kusa da cibiyar girgizar kasar.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta ce an samu karin tururin nukiliya a Onagawa a kusa da yankin da ambaliyar ruwan teku ta tsunami ta fi shafa ainun.

A halin da ake ciki kuma, an bayar da rahoton cewar abinci da ruwa da mai na yin karanci a wasu sassa na kasar ta Japan.