Ana ci gaba da kidaya kuri'a a Nijar

Ana ci gaba da kidayar kuri'a a Nijar Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Nijar, ana ci gaba da kidayar kuri'u bayan rufe rumfunan zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a kasar ranar Asabar.

An fafata ne tsakanin Alhaji Seyni Oumarou na jam'iyyar MNSD- NASSARA, da Alhaji Mahammadou Issoufou na jam'iyyar PNDS Tarayya.

Da misalin karfe shida da rabi ne dai na ranar Asabar din aka rufe rumfunan zaben a duk fadin kasar, kana aka fara kidaya kuri'a da misalin karfe bakwai.

Ana sa ran fitar da sakamakon zaben nan ba da dadewa ba.

Zaben dai ya gudana lafiya, kuma rahotanni na cewa galibi dai jama'a sun fito domin kada kuri'unsu.