G8 za ta tattauna game da takunkumi a Libya

Ministocin harkokin waje na kungiyar G8 za su tattauna a yau Talata a birnin Paris na kasar Faransa, game da rikicin dake faruwa a Libya.

A jiya Litinin ne dai Ministocin a wurin liyafar cin abincin dare, su ka fara tattaunawa akan wannan batu.

Kungiyar G8 dai ba kungiya ce da zata iya zartar da wani hukunci ba, kungiya ce da kawai za'a iya kawo ra'ayoyi da za'a iya amincewa akansu.

Sai dai kuma da wuya akan kai ga amincewa akan duk wani batu da ka iya tasowa a kungiyar.

Akwai alamar cewa har yanzu akwai sauran abubuwan da ke neman karin haske game da saka dokar haramcin hana zirga zirgar jiragen sama a Libya.

Tuni dai Birtaniya da Faransa suka rubuta wani daftari na kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ka iya amfani da shi.

Prime Ministan Birtaniya dai ya bayyana cewa lokaci na da matukar mahimmanci gare su, sai dai kuma har yanzu akwai rashin amincewa akan hanyar da ta kamata a bi wajen tabbatar da haka.

Nan da 'yan kwanaki kadan ne dai za'a yi wata muhawara a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

Tambayar da ke nan itace shin Birtaniya da Faransa; wadanda ke Allah- Allah wajen ganin an garkama dokar haramcin za su dauki matakin yin hakan idan kwamitin sulhun ya kasa cimma matsaya akai ko kuwa?