Fashewar makamashin nukiliya a Japan

Tashar nukiliya ta Fukushima Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An saken jin fashewar wani abu a Japan

An sake jin fashewar wani abu a tashar makamashin nukiliyar ta Fukushima a Japan wadda ta lalace sakamakon girgizar kasa.

An kuma ga wani hayaki ya tirnike sararin samaniya, sai dai ma'aikatan da ke kula da tashar nukiliyar sun ce sundukin da ke dauke da makamashin nukiliyar bai samu wata illa ba, sakamakon fashewar wani abin da a ka ji.

Kamfanin dillacin labaru na kasar Japan ya ce an gano gawarwakin mutane kimanin da dubu biyu a wasu yankuna biyu da ke gabar teku a lardin Miyagi da ke arewa maso gabashin kasar.

An kuma gano gawarwakin mutane dubu a Ojika da kuma wasu mutum dubu garin Minamisanriku wadanda ambaliyar ruwa ta tsunami ta shafe.