Mahamadou Issoufou ya lashe zaben Nijar

Mahamadou Issoufou
Image caption Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS shi ne jarogaran 'yan adawa

Hukumar zabe a Jamhuriyar Nijar ta bayyana jagoran 'yan adawa Mahamadou Issoufou, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 57 cikin dari.

Mr Issoufou ya sha kayi a zabuka biyun da su ka wuce a hannun tsohon shugaba Tandja, wanda sojoji suka kifar a bara.

Dan takarar jam'iyyar Tandja Seini Oumarou ya samu kashi 42 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Mutane kamar miliyan shidda da dubu dari bakwai ne aka ce sun kada kuru'arsu a zaben.

An shirya zaben ne domin maida kasar tafarkin Dimokuradiyya.

Tuni dai gwamnatin kasar Faransa wadda ta yiwa Niger din mulkin mallaka ta yi na'am da yadda aka gudanar da zaben na Jamhuriyar Niger.

A wani taron manema labarai da yayi, kakakin ma'aiaktar harkokin wajen kasar Faransa, Bernard Valero ya bayyana cewar Faransa ta yi na'am da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali a cikin nutsuwa ba tare da wata muna-muna ba.

Kakakin ma'aiaktar harkokin wajen ya bayyan cewar amincewa da wanann sakamakon zabe, yana da matukar muhimmanci wajen samun nasara kammala shirin sojoji na mika mulki ga hannun farar hulla, yana mai cewar kamata yayi abi hanyoyi wadanda doka ta tanada bisa sabon tsarin mulkin kasa, wajen yin duk wani kalubale akan wanann sakamako na wucin gadi idan har akwai.

Kawo yanzu dai jam'iyyar MNSD nasara wadda dan takararta ya sha kaye a zaben ba ta kai ga fitar da sanarwa ba a kan sakamakon ba.