Yansandan Najeriya sunce za su dakile duk wata barazanar kungiyar MEND

Rundunar yansanda a Najeriya ta ce a shirye take ta murkushe duk kanin wata barazana da wata kungiya za ta yi domin tayar da hankalin jama'a.

Rundunar na mayar da martani game da wata barazanar da Kungiyar fafitukar 'yantar da yankin Niger-Delta, wato MEND ta yi.

A cikin sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce, nan ba da dadewa ba za ta kai hare-haren bam a kan cibiyoyin da ake hakar mai da kuma wasu muhimman wurare a Abuja da Legas.

Kungiyar ta ce ta fusata ne sakamakon watsin da gwamnatin Najeriyar ta yi wajen kyautata rayuwar al`umar yankin Niger-Delta, tana mai zargin cewa shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya fi mai da hankali ne wajen kashe dukiyar kasar a kan 'yan banga a yakin neman zaben da yake yi.