Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsarin raba iko a tafarkin dimokuradiyya

Image caption Jama'a na kada kuri'a a zabukan fitar da gwani a Najeriya

Raba iko tsakanin Majalisar dokoki da bangaren zartarwa na daya daga cikin tanade-tanaden tsarin mulkin Demokradiyya, wato bangaren zartaswa ya kasance baya yiwa Majalisa da bangaren shari'a katsalandan.

Samun Majalisa ko bangaren shari'a da zai iya takawa bagaren zartaswa burki, a cewar masana wani muhimmin ginshiki ne a tsarin mulkin dimokradiyya. A jerin rohotanni na musamman da muke kawo muku akan zaben Nigeria dake tafe, inda za ku ji sharhi, hirarraki da shirye-shirye na musamman.

To anya kuwa a Nigeria wannan tsarin raba iko na aiki kamar yadda ya kamata?

Wannan shi ne batun da wakilinmu na Kaduna Nurah Ringim ya duba mana a wannan rohoto na musamman.