An kafa dokar ta-baci a Bahrain

Tashin hankali a Bahrain Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashin hankali a Bahrain

Akalla mutane biyu sun hallaka a Bahrain, kuma daruruwa sun jikkata, a lokacin artabun da aka yi tsakanin masu zanga zangar neman kafa demokradiyya a kasar, da kuma dakarun tsaro.

Ana kara samun rahotannin tashin hankali a yankunan mabiya darikar Shi'a.

A asibitin Salmaniya, likitoci na duba wadanda suka samu raunuka.

Likitocin sun shaida wa BBC cewa lamarin na neman fin karfinsu.

Tun bayan bayyana kafa dokar ta baci, 'yan Shi'a suka fara sanya shingaye a kan tituna da kuma daura damara, kan abin da suka kira jiran ko ta kwana.

A cewarsu, jami'an tsaron kasar na iya yin amfani da karfi domin dakile duk wata zanga-zanga.