Kwalara na hallaka jama'a a Ghana

Jama'ar kasar Ghana Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Jama'ar kasar Ghana

Gwamnatin Ghana ta ce cutar kwalara na cigaba da janyo hasarar rayuka a kasar.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma'aikatar lafiyar kasar tace daga watan Janairu zuwa yanzu, mutane 18 cutar kwalarar ta kashe daga cikin mutane sama da 700 da aka kwantar a babban asibitin koyarwa na kasar da ke birnin Accra.

Ma'aikatar lafiyar ta yi kira ga jama'a da su dauki matakan kariya daga cutar, ta hanyar tsabtace abincinsu da muhallinsu.

A cewar ma'aikatar lafiyar ta Ghana, ana kara samun hasarar rayuka a wasu yankunan kasar, sakamakon kamuwa da cutar kwalarar.