Damuwa akan tashar nukiliyar Japan

Tashar nukiliya a Japan Hakkin mallakar hoto nhk
Image caption Tashar nukiliya a Japan

Masu kula da tashar makamashin nukiliyar nan da ta lalace, a sakamakon girgizar kasa da mahaukaciyar ambaliyar ruwan da suka afkawa kasar Japan ranar Juma'a, sunce ana kokarin gyara yadda zaa ci gaba da sanyaya tukwanen tashar.

Hakan ya faru ne bayan fashewar da wasu abubuwa suka yi a tashar da kuma wutar da ta kama, wadda ta kara yawan tururin nukiliyar da ke bazuwa daga tashar.

Praministan Japan din, Naoto Kan, da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya sun bayyana damuwarsu, tare da yin kiran a samar da ingantaccen bayani akan lokaci.

Rahotanni akan yanayi na bayyana cewar, iskar da ake fama da ita a kasar, tana kwasar tururin nukiliya daga tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi, inda ta ke ketarawa da shi ta kan teku zuwa yankin gabashin kasar ta Japan.

Mutane fiye da miliyan guda ne yanzu suke zaune a sansanonin wucin gadi, inda kuma aka ce ana fama da karancin ruwa da abinci da kuma makamashi.