PDP ta gano makarkashiyar yin magudi

A Najeriya, Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, ta ce ta bankado wata makarkashiya da ake kokarin yi da nufin tafka magudin zabe a shiyyar kudu maso gabashin Kasar.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa, ana shirin yin amfani ne da wasu Jami'an hukumar zabe waje aikata magudin.

Har ma Jam'iyyar ta aika da wasikar koke kan wannan batu ga Shugaban hukumar zabe ta kasa.

Sai dai kuma mutane na mamakin ta yanda za'a ce Jam'iyyar PDP na kuka kan zargin tafka magudi, lamarin da wasu ke tunanin cewa watakila Jam'iyyar ta hango cewa za ta fadi zabe ne a Jihohin da ta ke mulki da ke shiyyar kudu maso gabashin Kasar.