Sojoji na karawa da masu zanga zanga a Bahrain

Zanga zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga zanga a Bahrain

Jami'an tsaro a Bahrain sun yi amfani da tankokin yaki, da barkonon tsohuwa, da motocin watsa ruwa, da helikwaftoci don korar daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati daga Dandalin Pearl da ke birnin Manama.

Wani jagoran 'yan adawa ya shaidawa BBC cewa an kashe akalla mutane biyar, kana daruruwan mutane sun sami raunuka - ko da yake babu wata majiya mai zaman kanta da tabbatar da haka.

An kuma kafa dokar hana yawo a sassa da dama na birnin.

Akwai bayyanan dake cewa asibitoci da dama sun daina aiki, abinda yasa a ke kula da wadanda suka samu raunuka a masallatai da kuma gidaje.

Akasarin jama'ar kasar dai 'yan Shi'a ne, sai dai gidan sarautar Khalifa dake mulki na bin tafarkin Sunna ne.

Bahrain ta na da mahimmanci sosai ta fuskar hada-hadar kudade a yankin. Akwai kuma sansani sojin Amurka mai girma a kasar.