Kotu ta tabbatar da zaben majalisar dokokin Nijar

Alhaji Mahamadou Issoufou, zababen shugaban Nijar
Image caption Alhaji Mahamadou Issoufou, zababen shugaban Nijar

Kotun tsarin mulkin jamhuriyar Nijar ta tabbatar da sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

A ranar 31 ga watan Janairun da ya wuce ne aka yi zaben.

Kotun ta amince da zaben 'yan majalisa 107 daga cikin 113.

An soke zaben 'yan majalisar da aka gudanar a jahar Agadez saboda wasu dalilan da suka shafi yin magudi.

Nan da watanni biyu ne hukumomin kasar zasu sake gudanar da zaben a wannan jahar.