Seini Oumarou ya amince da zaben Mahamadou Issoufou

Alhaji Seini Oumarou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabon jagoran 'yan adawan Nijar

A jamhuriyar Nijar, dan takarar kawancen jami'yyun ARN, wanda ya fadi a zaben shugaban kasa da aka yi a karshen mako, Alhaji Seini Oumarou ya ce ya amince da sakamakon zaben.

Ya kuma jinjina ma abokin hamayyarsa na siyasa, sabon zababben shugaban kasar ta Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou, wanda ya asmu goyon bayan kawancen jam'iyyun CFDR.

A na shi bangare, sabon shugaban ya ce zai baiwa 'an hamayya, har ma da 'yan jarida hakkokinsu, kamar yadda tsarin mulki ya yi tanadi.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Alhaji Mahamadou Issoufou, ya samu kashi 57.95 daga cikin dari, yayinda kuma Alhaji Seini Oumoarou ya samu kashi 42.05 daga cikin dari.niger