'Yan sandan Jihar Ribas a Najeriya sun shiryawa zabe

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, yayin da zabukan Kasar ke ci gaba da karatowa, rundunar 'yan Sanda a Jihar Ribas da ke shiyyar Kudu Maso Kudancin Kasar, ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin tunkarar zabukan, tare da tabbatar da tsaro a lokacin zabe.

Jihar Ribas dai na daga cikin jihohin yankin Niger/Delta mai arzikin man fetur inda ake samun aiyukan masu tada kayar baya a can.

A baya- bayan nan ma sai da kungiyar MEND mai fafutukar kwato 'yancin yankin Niger/Delta ta ce za ta kai hare- hare a Jihohin Lagos da Abuja.

Akan haka ne rundunar 'Yan Sandan Jihar ta Ribas, ta fara gudanar da horon sanin makamar aiki ga Jami'anta.

Wannan horon dai ya hada da yadda za su tafiyar da ayyukan tsaro a yayin da ake gudanar da zabe a Kasar.

Rundunar 'Yan Sandan ta bayyana cewa wannan horon ya hada da yadda zasu bullowa zabukan watan Afrilu, domin ganin cewa zaben ya tafi lafiya. Rundunar ta bayyana cewa an kara yawan 'yan sandan sintiri a kan titunan Jihar.