Kwamitin Sulhu zai kada Kuri'a akan Libya

Hakkin mallakar hoto AFP

Magoya bayan kudurin Kwamitin Sulhu kan tabbatar da dokar haramcin zirga zirgar jiragen sama a Libya na son a kai ga kada kuri'a akan lamarin a yau dinnan, kafin dakarun Kanal Gaddafi su sake kai hari a garin Benghazi inda 'yan adawa ke rike da iko.

Sai dai kawo yanzu kan mambobin Kwamitin Sulhun na rarrabe akan ko shin shiga tsakani zai yi kyakkyawan tasiri ko a'a.

Bayan shafe tsawon lokaci anan tattaunawa, Amurka ta fito ta bayyana matsayarta akan saka dokar haramcin hana zirga zirgar jiragen sama a Libya.

A karshe jakadar Amurka a majalisar dinkin duniya Susan Rice ta bada tabbacin cewa Amurka ta amince da haka.

Sai dai ta bayyana cewa wannan ba zai wadatar ba wajen kare rayuwar bil adaman da ake kaiwa hari.

Don haka tana bukatar kwamitin ya dauki tsauraran matakai a kudurin da zai fitar.

Duk da dai ba ta yi karin haske akan wannan jawabi ba, sai dai Jakadun Kwamitin Sulhun sun ce ba za su amince da kai wa dakarun Libya dake kasa hari ta sama ba.

Wannan kuma na daya daga cikin abubuwan da ake takaddama akai.

Su dai kasashe masu cikakken ikon kada kuri'a a kwamitin kamar irin su Russia da Sin na shakkar duk wani nau'in amfani da karfin soji a kasar.

Wasu kasashen kuwa sun bayyana cewa sam ba za su so a tsunduma su cikin yakin basasar da ake yi ba.

Birtaniya kuwa da sauran masu rajin tabbatar da daukar mataki a kan kasar ta Libya sun bayyana cewa ba bu wanda ya isa ya iya dakatar da saka dokar haramcin zirga zirgar jiragen sama a kasar, tun da dai kungiyar kasashen Larabawa ce ta bukaci haka.

Sannan kuma sun jaddada mahimmancin tabbatar da wannan doka kafin dakarun Kanal Gaddafi su sake kai wani harin a garin Benghazi in da 'yan adawa ke rike da ikon sa.