Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ayyukan wayar da kai a karkara

Hakkin mallakar hoto AFP

Najeriya kasa ce dake kunshe da kungiyoyi masu zaman kansu da dama, cikin ayyukan da wasu daga cikin kungiyoyin kance suna yi shine na kokarin wayar da kan jama'a a bisa harkokin da suka shafi siyasar kasar na gudanar da zabe na gari domin samun shugabanni na gari.

To amma duk da ikirarin wadannan kungiyoyi, wasu a Najeriya sun sha nuna cewa kungiyoyin na gudanar da ayyukansu ne a birane, inda sukan bar mutanen karkara cikin duhu.

To ko me yasa irin wadannan kungiyoyi basu cika lekawa karkara ba don ayyukan wayar dakai? Daga kaduna ga rahoton da wakilinmu Nurah Mohammed Ringim ya hada mana rahoto. A yi sauraro lafiya