Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalolin da nakasassu ke fuskanta a lokacin zabe

A Nigeria alkaluma na nuna cewa akwai nakasassu kimanin miliyan 20 a kasar wadanda sama da miliyan goma daga cikinsu sun kai shekarun yin zabe.

Sai dai kungiyar kungiyar na koka cewa da dama daga cikinsu basa samun damar gudanar da zabukan tamkar dai yadda sauran yan kasar da basu da nakasa kan samu cikakkiyar damar.

Hakan ta kai ga har said a kungiyar ta gana da hukumar zaben kasar mai zaman kanta dan lalubo hanyoyin magance matsalolin da naksassun ke fuskanta a yayin zabuka.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya duba irin matsalolin da nakasassun ke fuskanta, sannan kuma ko hukumar zaben kasar ta yi musu wani tanadi na musamman a zabukan da ke tafe.