Masu ceto na kokarin gyara tashar Nukiliya a Japan

Tashar Nukiliya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashar Nukiliya a Fukushima

Ma'aikatan ceto a Japan suna cigaba da aikin shimfida wasu sabbin wayoyin lantarki zuwa na'urorin da ke sanyaya tukwannen tashar sarrafa makamashin nukiliya ta Fukushima.

Tashar ta Fukushima ta lalace ne a sakamakon girgizar kasar da aka a makon jiya.

Wani jami'i a Tashar ya ce matakin farko na daidaita al'ammura a tashar shine tabbatar da an samu wutar lantarki.

A halin da ake ciki kuma, Amirka ta bada sanarwar wani shiri na kwashe dubban 'yan kasarta daga Japan din yayinda aka gargadi 'yan Birtaniya da 'yan Australia da su fice daga kasar.

Su dai wadanda Amurka za ta kwashe, suna zaune ne a Honshu inda Amurka take da sansanin soja da na ruwa.

Amurkan ta ce yawancin mutanen za a kwashe sune da jiragen sama na 'yan kasuwa da kuma wadanda aka dauka shata, idan kuma akwai bukata, ayi amfani da jiragen soji na sama.