Dakarun Gaddafi na fuskantar cikas akan hanyar Benghazi

Yakin Libiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yakin Libiya

A Libiya, ga alama 'yan tawaye a gabashin kasar sun katse hanzarin sojojin gwamnati a garin Aj-dabiya, a yunkurinsu na dannawa zuwa birnin Benghazi.

Sai dai wasu rahotanni na cewa, dakarun dake biyaya ga Kanar Gaddafi suna shirin kai wani harin.

Masu aiko da rahotanni daga yankin sun ce, 'yan tawayen sun yi amfani da muggan makamai da kuma akalla jirgin sama na yaki guda, don tilastawa sojojin gwamnati janyewa daga garin na Aj-dabiya.

Garin shi ne ya rage a hannun 'yan tawayen a gabashin kasar, kuma yana kan hanyar zuwa birnin Beghazi ne.

Jiya kungiyar agaji ta Red Cross ta ce za ta janye daga Benghazi, saboda fargabar harin da aka ce sojojin gwamnati za su kai.

Amirka tace zata goyi bayan saka takunkumin da zai killace sararin samaniyar Libiya, kuma ta yi kira ga majalisar dinkin duniya ta dauki karin matakai masu tsauri.