'Yan adawa a Najeriya sun kasa kalubalantar PDP

A Najeriya an dade ana zargin Jam`iyyun adawar Kasar da kasa yin katabus wajen kalubalantar Jam`iyyar PDP wadda ke mulkin Kasar.

Cikin shekaru goma sha biyu da Kasar ta yi da komawa ga turbar demokradiyya, Jam'iyyar ta PDP ce ke mulkin Kasar.

Jam`iyyun adawar sun yi yunkuri daban- daban da nufin kulla kawance da juna don tunkarar Jam`iyyar PDP, amma ba su kai ga cimma wata kwakkwarar matsaya ba.

Wannan kuma ya faru ne a sakamakon wasu bambance- bambancen da ke tsakaninsu, irin na akida da kuma zargin da ake yi wa wasu na son zuciya.