Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin Abobo

Tashin hankali a Abobo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashin hankali a Abobo

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, tayi Allah wadai da harin da aka kaiwa wata kasuwa a birnin Abidjan.

Akalla mutane 25 ne suka hallaka, a harin da aka kai a kasuwar Abobo, daya daga cikin unguwannin da ke goyon bayan Alassane Ouattara, mutumen da kasashen duniya suka ce shine ya lashe zaben shugaban kasar na watan Nuwambar da ya gabata.

Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakin kai wannan hari akan sojojin da ke biyayya ga Laurent Gbagbo.

A nata bangaren, kotun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, ECOWAS ko CEDEAO, ta hana kungiyar yin amfani da karfin soja waje warware rikicin siyasar Cote d'Ivoire.

Umurnin kotun da ke zama a Abuja dai na wucin-gadi ne, har ya zuwa lokacin da za a gama sauraron wata kara da aka shigar a gabanta.

Lauyan shugaban Cote d'Ivoire mai ci a yanzu ne, watau Laurent Gbagbo ya shigar da karar, inda ya ke kalubalantar matsayin da Ecowas ta dauka, a lokacin wani taron da ta yi a Abuja, a kan rikicin siyasar kasar ta Cote d'Ivoire.