Rikicin kasar Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption wasu magoya bayan Alasan Qautttara a Ivory Coast

Kungiyar Kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira da kakkausar murya ga dakarun dake biyayya ga Laurent Gbagbo wanda yaki amincewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a Ivory Coast, da su dakatar da hare-haren da suke kaiwa kan magoya bayan Alasan Qauttara.

Wannan kira ya zo kwana biyu bayan da dakarun Laurent Gbagbo suka kai hari a wata kasuwa a yankin Abobo a birnin Abidjan, inda aka kashe akalla mutane 20 tare da raunata wasu kimanin sittin.

A wata sanarwa da mataimakin directa na kungiyar Borenick Obert ya fitar, ta ce jami'an tsaron da ke irin wadanan hare hare wajibi ne su dakatar da duk wani abu da zai haifar da asarar rayukan jama'a.

Magoya bayan Mr Alasan Quattara mutumin da kasasahen duniya suka ce shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan nuwamban bara, sune suka fi rinjaye a wurin da lamarin ya auku.