A yau shugabannin duniya zasu yi taro kan Libya

.

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Mr David Cameron

A yau shugabannin kasashen duniya zasu gudanar da wani taro a birnin Paris na kasar Faransa kan matakin soji da za'a dauka kan kasar Libya

A jiya ne dai Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce ya zaman wajibi ga Kanar Ghaddafi ya dakatar da kai hare-hare akan fararen hula, matukar yana son kaucewa daukar martani soji daga kasashen duniya, biyo bayan kudirin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar a ranar alhamis data gabata.

Hakazalika ita ma fadar Downing street a Burtaniya, ta fitar da wata sanarwa a jiya inda ta ja kune kanar Gaddafi kan bukatar ganin cewa ya janye dakarunsa , ya kuma maida wutar lantarki da ruwan pampo a garuruwa da yake fada da su.

Ta kuma bukace shi da ya daina budewa fararen hula wuta.

Firaministan Burtaniya David Cameron , na cikin shugabannin da zasu halarci taron da za'a gudanar.