An kafa dokar ta baci a Yemen

Ali Abdullah Saleh Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ali Abdullah Saleh

Shugaban Yemen, Ali Abdullah Saleh, ya kafa dokar ta baci bayan an kashe kusan mutane arba'in, wadanda suke zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a babban birnin kasar, Sanaa.

Rahotanni sun ce, sojojin da suka labe a rufin gidaje, sun yi harbi kan jama'a, bayan an kammala sallar Juma'a.

Amirka da Tarayyar Turai sun yi tir da tashin hankalin.

Shugaba Barack Obama yayi kira ga takwaran aikinsa, Ali Abdullah Saleh, da ya bari a yi zanga-zangar lumana a kasar.

Masu zanga zangar suna bukatar shugaba Ali Abdullah Saleh yayi murabus, bayan ya kwashe fiye da shekaru 30 yana mulkin kasar.