Dakarun kasashen yammaci sun kai wa Libya hari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani wuri da aka kaiwa hari a Libya

Kasashen yammaci sun kadamar da hare hare ta sama da kuma harba makamai masu linzami a'kan kasar Libya domin aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na hana zirga zirgan jiragen sama da kuma hana dakarun kwanel Gaddafi kaiwa farar hula hari.

Ma'aikatar tsaro ta Faransa a birnin Paris ta ce jiragen saman sojin kasar ne suka fara kaiwa Libya hari.

Amurka ta ce sojin jiragen ruwan kasar da kuma na Birtaniya sun harba bamai bamai masu linzami fiye da dari daya kan wuraren da ake adana kayan yakin sojin libya.

Firaministan Birtaniya David Cameron, ya sanar cewa dakarun kasar sun fara daukar mataki a sararin samaniyar Libya

Sai dai shugaba kwanel Gaddafi na Libya ya ce dakarunsa zasu maida martani akan makiyansu.

A wani jawabin da ya gabatar a wata kafar talibijin ta gwamnatin kasar, Mr Gaddafi ya yi barazanar kaiwa kasashen dake kusa da tekun Mediterranean hari.

Kamfanin dilancin labaru na Reuters ya ce anyi ta jin karar bindigogi dake harbin jiragen sama da sanyin safiyar yau, a birnin Tripoli babban birnin kasar.