An amince da gyaran tsarin mulki a Masar

Zaben raba-gardama a Masar Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Zaben raba-gardama a Masar

Jami'ai a Masar sun ce masu zabe sun kada kuriar amincewa da sauye-sauyen da aka yi wa tsarin mulkin kasar.

Miliyoyin jama'a ne dai suka fito don kada kuri'a jiya Asabar, makonni 5 bayan jerin zanga-zangar da aka yi, wadanda suka kai ga hambarar da shugaba Hosni Mubarak.

Amincewa da sabon kundin tsarin mulkin, zai share fagen mika mulki ga wata gwamnatin farar hula a cikin 'yan watanni masu zuwa.

Ana sa ran gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a cikin watan Satumba, da na shugaban kasa a karshen shekara.

Sai dai wasu shugabanni da suka jagoranci jerin zanga-zangar sun yi korafin cewa, sauye-sauyen da aka yi a cikin kundin tsarin mulkin, ba su cika ka'idojin demokradiyya ba.

A cewar su kuma, jaddawalin zabubukan, bai ba jam'iyyu isasshen lokaci na shiryawa ba.