Kasashen yamma na cigaba da kai hare hare a Libiya

Harin kasashen kawance a Libiya Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Harin kasashen kawance a Libiya

Amirka ta ce, jiragen samanta na yaki sun kaddamar da sabbin hare-hare akan dakarun Kanar Gaddafi na Libiya, da kuma wuraren da kasar ta girke na'urorinta na kare sararin samaniya.

Kamar yadda Admiral Mike Mullen, jami'in soja mafi girma a Amirka ya ce, sun yi nasara a hare-haren farko da suka kaiwa Libiyar, kuma dakarun Gaddafi sun daina nausawa zuwa Benghazi.

Masu aiko da rahotanni a Libiyar sun ga tankunan yaki da sauran motocin soja da suka kone.

A daren jiya ne kasashe da suka hada da Amirka da Birtaniya da kuma Faransa, suka soma kaiwa Libiyar hare-hare, bayan da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya amince da hakan, a wani mataki na neman kare fararen hula a kasar.

Rasha ta yi kira ga kasashen da su daina kai hari akan wuraren da ba na soja ba. Ta ce hare-haren na rutsawa da fararen hula.

Sakataren kungiyar kasashen Larabawa, Amr Moussa, ya ce an wuce makadi da rawa a hare-haren na neman hana jiragen sama yin shawagi a sararin samaniyar Libiya.

A nasa bangaren, jagoran Libiyar, Kanar Gaddafi, ya ce hare-haren na ta'addanci ne, kuma ba zasu yi wani tasiri ba.