Rundunar sojan Libiya ta yi shelar daina bude wuta

Harin sojan kawance a Libiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin sojan kawance a Libiya

Rundunar sojan Libiya ta yi sanarwar dakatar da bude wuta nan take, a daidai lokacin da dakarun kasashe ke cigaba da kai mata hare-hare.

Amirka da Faransa sun ce, kasar Qatar za ta shiga cikin farmakin da kasashe ke kaiwa Libiya.

A cewar jami'an Faransa, Qatar din tana shirin tura jiragen sama guda hudu.

Tun kamin nan dai sakataren kungiyar kasashen Larabawa, wadda tana daga cikin masu goyon bayan daukar matakin soja a kan Libiyar, ta ce an wuce gona da iri a hare-haren da ake kaiwa Libiyar.

Kamar yadda Amr Moussa ya ce, abinda suke so shine a kare fararen hula, ba wai a kara kai masu hare-hare ba.

Ita ma Rasha ta yi kira ga Birtaniya da Faransa da kuma Amirka, da su daina kai hari akan wuraren da ba na soja ba.

Rashar ta ce, hare-haren na rutsawa da fararen hula.

Da yammacin yau gwamnatin Libiyar ta ce dakarunta za su dakatar da bude wuta nan take.

Wani kakakin gwamnatin Libiyar, Ahmed al Sharif, ya kuma gayyaci al'ummar Libiya da su halarci wani maci na zaman lafiya, daga Tripoli zuwa birnin Benghazi.